31 Maris 2026 - 22:46
Source: ABNA24
Yadda Kasashen Larabawan Tekun Farisa Suka Matsawa Amurka Lamba Don Ci Gaba Da Yaƙi Kan Iran

Kasashen Larabawa na Tekun Fasha, musamman Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, suna ci gaba da karfafa Amurka wajen ci gaba da yaki kan Iran. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ba da rahoton cewa, galibin kasashen Larabawa na yankin Gulf na goyon bayan ci gaba da yakin da ake yi da Iran; Burinsu shi ne samar da sauye-sauye masu tushe da asali a manufofin siyasar Iran. 

Wasu daga cikin wadannan kasashe ma sun goyi bayan zabin kai hare-hare da ayyukan kasa kan Iran, inda suka bayyana shi a matsayin wani lokaci mai cike da tarihi na kawo karshen gwamnatin Iran. A cewar rahoton, ya nakalto jami'an Amurka, Isra'ila da kasashen Larabawa, kawayen Amurka a yankin Takun Farisa karkashin jagorancin Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa suna karfafa gwiwar shugaban Amurka Donald Trump da ya ci gaba da yaki da Iran. Sun yi imanin cewa Iran ba ta yi rauni sosai ba bayan ɗaukar wata guda da hare-haren jiragen sama na Amurka suka kai ƙasar. 

Rahoton ya kuma ambato jami'ai na cewa, a yanzu wasu kawayen yankin na kallon lamarin a matsayin wata dama mai tarihi ta kawo karshen mulkin Malaman kasar gaba daya a Iran. 

Jami'ai daga Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait da Bahrain sun bayyana a cikin tattaunawar sirri cewa ba sa son dakatar da ayyukan soji kafin samar da sauye-sauye a shugabancin Iran ko kuma wani gagarumin sauyi a yanayinta. 

Donald Trump ya kuma shaida wa manema labarai a baya-bayan nan cewa: "Saudiyya na gwagwarmaya sosai, Qatar na yaƙi matuƙa, UAE itama na yaki, Kuwait na yaƙi kuma Bahrain ma na yaki ... duk suna da hannu". Duk da wannan goyon baya na gaba ɗaya, akwai bambance-bambance tsakanin ƙasashen Larabawa na Tekun Farisa. Yayin da Saudi Arabia da UAE ke son ƙara matsin lamba na soja - Ita kuma UAE tana da matsayi mai tsauri kuma tana goyan bayan harin ƙasa (zabin da Kuwait da Bahrain ke marawa baya) - akasin haka, Oman da Qatar sun fi so, sun fi karkata ga matsayinsu na yau da kullum na matsayin mai shiga tsakani tsakanin Iran da ƙasashen da bin hanyoyin diflomasiyya. 

Daga mahangar Saudiyya, kawo karshen yakin da ake ciki a halin da ake ciki ba zai haifar da kyakkyawar yarjejeniya da za ta tabbatar da tsaron kasashen yankin ba. Riyadh ta jaddada cewa, duk wata yarjejeniya dole ne ta hada da kawo karshen shirin nukiliyar Iran, da lalata karfin makami mai linzami na Iran, da kuma tabbacin cewa ba za a rufe mashigar Hormuz nan gaba ba. 

Fadar White House ta ki cewa komai kan rahoton, inda ta bayyana cewa, Amurka da kawayenta a Tekun Farisa sun tabbatar da cewa bai kamata a bar Iran ta mallaki makamin nukiliya ba. Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ya shaida wa jami'an Amurka cewa raunana karfin sojojin Iran zai anfanar a cikin dogon lokaci a yankin. 

Sai dai har yanzu Saudiyya na yin taka-tsan-tsan game da tsawaita yakin, saboda ta damu da kai hari kan cibiyoyin man ta.

Tunatarwa: waɗannan duk faɗi tashi maras amfani ne ga waɗannan ƙasashe da suka rasa me za su yi. Wanda ba abun da ba su yi ba babu abinda anan gaba kuma da zasu iya don hana ci gaban Iran karya suke ba makamai masu linzami ko Nukiliya ne matsalar su kawai musulunci da musulmin Iran ne matsalarsu.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha